TSARIN HAKIMAI DA AIKINSU DA KIRARINSU
.
KASHI NA TAKWAS (8)
.
MARDANNIN ZAZZAU
Sarautar Mardanni, sarauta ce wadda ta sami asali daga sarautun Habe kuma ana ba da wannan sarauta ce ga mace a wancan lokaci, ko diyar Sarki ko kanwar Sarki ( Babba ) to, amma a lokacin Fulani an sami haka amma ba a kara ba, daga kan wadda aka yi wa wannan sarauta ta Mardanni. An mai da wannan sarauta zuwa saravar 'ya'yan Sarki maza a zamanin Sakin zazzau na biyu Malam Yamusa a Daular Fulani. Wannan sarautana daya daga cikin sarautu ta 'Ya'yan Sarki a zazzau. Wadda ta fara wannan sarauta ita ce Mardanni A'i diyar Musa Sarkin Zazzau. Mardanni na aiki ne a kan tausasa sarki a kan harkokin da suka shafi Daji ko cikin Gida amma lokacin da maza suka fara yana cikin gida.
.
=== KIRARIN MARDANNI ===
YANKA DAMISA SHIGAYYA KWANDO,
SHIGAYYA KWANDO YANKA DAMISA,
MARDANIN SARKI DAN UBAN GABASAWA.
Wannan shi ne kirarin Mardannin zazzau ana kuma nuna irin kokarinsa da jaruntakarsa.
.
MAGATAKARDAN ZAZZAU
Sarautar Magatakarda tana daya daga cikin sarautar Habe da har yanzu ake amfani da ita bisa tsarin yadda take. Sarauta Magatakarda a lokacin Habe tana cikin Rukunin sarauv na Malamai ne kuma aikin Magatakarda a wancan lokaci na Habe shi ne kamar mai wa'azi na gidan Sarki kuma shi ne ke fadin sakamakon binciken abin da zai faru in an shiga sabuwar shekara.
.
Sarautar Magatakarda a lokacin Mulkin Fulani ta canja, sì ne ke karban takardar sako tsakanin kasa da kasa ko Sarki da Sarki haka kuma shi ke rubuta takardar sako da abin da ya shafi rubuce-rubucen fada. Kuma shi ne ke gaba da kowa a tsarin zaman majalisa, saboda shi ne ke yi ma Sarki bayanin aiki da abin da majalisa ko masaravar ta kunsa a gaban Sarki, amma yanzu akwai 'yan canje-canje. Magatakarda na nan a kan aikinsa na gcatar da tsare-tsaren aiki na yau da kullum a gaban sarki, sai dai ba shi ke jagoranta ba kamar da yadda sarautar take.
.
=== KIRARIN MAGATAKARDA ===
UBAN MAKARANTA,
MAGATAKARDAN SARKI
ZA NA TAKARDU ZANCEN SARKI,
Wannan shi ne kirarin Magatakarda inda aka nuna matsayinsa a da, da yanzu (Lokacin mulkin Habe da na Fulani)
.
SARKIN YAMMAN ZAZZAU
Saravar Sarkin yamma na daya daga cikin sarautun Habe a kasar zazzau. Wannan sarauta ce ta Hakimci mai kula a bangaren Yamma, sarauta ce da ake ba dan Sarki kowani muhimmin mutum. Wanda aka fara nadawa shine Alh. Tanimu Tankon Mama a matsayin sarkin Yamman zazzau. A lokacin Mulkin Fulani a zazzau cikin zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris.
.
=== KIRARIN SARKIN YAMMA ===
SARKIN YAMMAN SARKI,
SARKIN YAMMAN DODO,
SARKIN YAMMAN UBAN GABASAWA
.
SARKIN KUDUN ZAZZAU
Sarautar Sarkin Kudu sarava ce wadda ta kafu a lokacin Mulkin Fulani, tana daya daga cikin sarautu hudu da aka kasa, Gabas Yamma, kudu da Arewa. Wannan sarauta ce ta Hakimci, mai kula da bangaren Kudun Wannan sarauta ana ba Dan Sarki ko wani muhimmi a kasa. Amma a nan zazzau a nan zazzau wanda ya fara yin wannan sarauta shi ne Malam Sambo Shehu Idris dan Sarkin zazzau Shehu Idris.
.
=== KIRARIN SARKIN KUDU ===
�SARKIN KUDUN SARKI
DARZAZA KATANGAR GISHIRI
TSAKIYA DA RUMBUN HATSI
NI'IMA A BAKIN KOFA
SARKIN KUDUN SARKI
DAN UBAN GABASAWA.
.
KARIN BAYANI: Tarihi ya tabbatar da ba a nada Sarkin kudu ba a zazzau lokacin Mulkin Habe sai a lokacin Mulkin Fulani a lokacin Mulkin Fulani ma ba a nada ba sai cikin Mulkin sarkin zazzau Shehu Idris, saboda akwai wakilin kudu a wancan lokaci da kuma Ma'ajin zazzau Karami wanda shi ne wakilin Sarki kuma Hakimi a kudancin Kasar zazzau.
.
SARKIN AREWAN ZAZZAU
Wannan Sarauta ta Sarkin Arewa, sarava ce da ta kafu a karkashin Daular Fulani a zazzau kuma wannan saravan daya daga cikin sarautu hudu da aka kasa su kamar haka Gabas Yamma, kudu da Arewa. Wadannan Hakimai su kula da bangare hudu na kasa tare kuma da wakilai a karkashin wannan sarauta. A na ba dan Sarki kowane muhimmin mutum. Wanda ya fara sarauta ta Sarkin Arewa shi ne Malam Suleimanu Magatakarda daga gidan Gidadawan zazzau.
.
=== KIRARIN SARKIN AREWA ===
SARKIN AREWAN SARKI,
SARKIN AREWA DODO,
SARKIN AREWA UBAN GABASAWA
Wannan shi ne kirarin Sarkin Arewan Zazzau.
.
KOGUNAN ZAZZAU
Sarautar Kogunan zazzau na daya daga cikin Sarautu da Fulani suka aro a wannan lokaci na Sarkin zazzau Alhaji Shehu Idris, kuma sarauta ce da aka fara nada ta a kan dan Sarki. Wannan rarauta ta koguna ana ba da ita ga dan sarki kowane amintaccen mutum a kasar zazzau. Wanda yafara wannan sarauta shi ne Mal. Muhammadu Nura Aminu dan Sarkin zazzau Muhanadu Aminu.
.
=== KIRARIN KOGUNA ===
KOGO DA ARZIKI A CIKINSA
KOGUNAN SARKI,
KOGO HIRA KOGO TSIRA
KOGUNAN DAN UBAN GABASAWA
.
SARKIN DAWAKIN TSAKAR GIDA
Wannan sarauta ta Sarkin Dawakin tsakar Gida tana daya daga cikin Sarautun da aka aro. An fara nada ta a zamanin Mulkin Sarkin zazzau Alh. Shehu Idris. An Kuma nada ta ne a kan Dan sarki a wannan zamani na Mulkin Fulani. Wanda ya fara wannan sarauta shi ne Malam Ibrahim Idris, dan Sakin zazzau Shehu idris
KIRARIN SARKIN DAWAKIN TSAKAR GIDA
MAI TSAKAR GIDA
SADA UMURNIN SARKI
ALKAWARI GA MAI DAKI
SARKIN DAWAKIN TSAKAR GIDAN SARKI
DAN UBAN GABASAWA
Wannan shi ne kirarin Sarkin Dawakin tsakar gida.
.
SARKIN GABAS ZAZZAU
Wannan sarauta ta Sarkin Gabas ita ma sarauta ce da a kafu a a karkashin Daular Fulani. Ita ma tana cikin sarautun Hakimci mai kula da gabashin kasa don aikin sarki. Wannan sarauta ana ba dan Sarki ko kowane muhimmin mutu. Wanda ya fara wannan sarauta shi ne Malam Musa Auchan, cikin zamanin mulkin sarkin Zazzau Shehu Idris
.
=== KIRARIN SARKIN GABAS ===
SARKIN GABAS DIN SARKI
SARKIN GABAS DIN DODO
SARKIN GABAS DIN UBAN GABASAWA
Wannan shine kirarin sarkin Gabas din zazzau.
0 Comments