TSARIN HAKIMAI DA AIKINSU DA KIRARINSU (10)

TSARIN HAKIMAI DA AIKINSU DA KIRARINSU
.
KASHI NA GOMA (10)
.
52. DURBIN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Durbi tana cikin sarautu da aka aro ta , a wannan zamani na Daular Fulani. Wannan sarauta ce ta 'ya'yan sarki yanzu a zazzau. An fara nada ta a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris. Wanda aka fara nadawa shi ne Malam Aliyu Umaru, jikan Madaki Yero, dan Sarkin zazzau Alu dan sidi, na gidan Mallawa.
..
== KIRARIN DURBI ==
DURBIN SARKI,
DURBIN DODO
DAN UBAN GABASAWA.
.
53. SARKIN BAURAN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Sarkin Baura tana daya daga cikin sarautu da aka aro ta a wannan zamani na Mulkin Fulani kuma sarauta ce da aka fara nada ma dan Sarki kuma yanzu tana daya daga cikin sarautun 'ya'yan Sarki. An fara nada ta a zamanin Sarkin zazzau shehu Idris. Wanda aka fara nadawa shi ne Mal. Hayatu dan Ciroman zazzau Mal. Muhammadu Hayatuddin na gidan Barebari.
.
== KIRARIN SARKIN BAURA ==
SARKIN BAURA SARKI,
SARKIN BAURAN DODO,
SARKIN BAURAN UBAN GABASAWA
DAN UBAN GABASAWA.
.
54. BUNUN ZAZZAU
Sarautar Bunu na daya daga cikin sarautun da aka aro ta a wannan zamani na Mulkin Fulani, kuma sarauta ce ta 'ya'yan Sarki yanzu a zazzau. An fara nada ta a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris. Wanda aka fara nadawa shi ne Mal. Sidi yero dan uban Doman zazzau na gidan Mallawa.
.
==  KIRARIN BUNU  ==
BUNUN SARKI
KI JIKI DOMIN SARKI,
KI JIKI DOMIN ZAKI
BUNU BAIBAYAN GARI,
DAN UBAN GABASAWA
Wannan shi ne kirarin Bunun zazzau.�

.
55. DAN DARMAN ZAZZAU
Wannan Sarauta ta Dangaladima tana cikin sarautun da aka aro a cikin wannan zamani na Mulkin Fulanh, kuma sarauta ce wadda aka fara nadawa  dan Sarki. Yanzu tana daya daga cikin Sarautun 'ya'yan Sarki a zazzau. An fara yin ta lokacin sarkin zazzau Shehu Idris. Wanda aka fara nadawa shi ne Malam Zailani Ibrahim na gidan Barebari. Kuma daya daga cikin jikokin Kauru Idris, dan Yamusa Sarkin zazzau.
.
=== KIRARIN DAN DARMAN ===
DAN DARMAN DAN SARKI
DAN DARMAN DODO
DAN DARMAN UBAN GABASAWA
.
56. JAKADAN ZAZZAU
Wannan Sarauta ta jakadan zazzau Sarauta ce wadda ta samo asali tun lokacin Mulkin Habe. Wannan sarauta ta Jakada tana daya daga cikin manyan sarautun Yaran Sarki. A wancan lokaci, shi ne ke matsayin Babban manzo tsakanin kasa da kasa a kan kowace irin hidima da ta taso, kamar yaki da ziyara da aure. Wannan sarava ta Jakada an karrama ta lokacin Mulkin Fulani ta zama sarauta ta Hakimci mai matsayi. Wanda ya fara wannan sarauta ta Jakada shi ne Ja kada Usman, a zamanin Sarkin Zazzau Malam Musa.
.
===  KIRARIN JAKADA ===
JAKADAN SARKI,
KA TAFI DA GASKIYA,
KA DAWO DA AMANA,
KA TABBATAR DA HAKIKA.
.
57. MATAWALLIN ZAZZAU
Sarautar Matawalli sarauta ce cikin sarautun da aka aro a wannan Lokaci na Mulkin Fulani, wannan sarauta ana ba da ita ne ga mutum mai ilimi kamar yadda ake ba da sarautar Salanke da Wali, to, wannan sarauta ma na cikin wannan rukuni. An fara nada ta a lokacin Sarki Ja'afaru da aka nada Matawalle Malam Muhanadu Aminu na Unguwar Juma. " Matwaf Mal" kalmar Larabci ce, ma'ana Mai kula da " Beit Mal" Baitulmali, wata
ma'ajiyan kudi na Hukuma. An aro ta daga Masarautar Katsina.
.
=== KIRARIN MATAWALLI ===
MAI BAITIL MALI,
MATAWALLIN SARKI,
MAI DUKIYA DA MVANE
MUTAWALLIN DODO
MUTAWALLIN UBAN GABASAWA.

Post a Comment

0 Comments