TSARIN HAKIMAI DA AIKINSU DA KIRARINSU
.
KASHI NA SHA DAYA (11)
.
58. DAN AMAR ZAZZAU
Wannan sarauta ce da ake ba 'ya'yan Sarki a Kano kuma tana da tarihi mai yawa a kanta. Sarautar Dan Amar tana cikin Sarautun da aka aro a cikin sarautu na zamanin Mulkin Fulani. Wannan sarauta ce da ake ba mahimmin mutum a gari, kuma sarauta ce ta hakimci mai girma yanzu a wannan masarauta ta zazzau. An fara nada ta a zamanin Sarkin Zazzau Shehu Idris. Wanda aka fara nadawa shi ne Mal. Badamasi Aliyu a matsayin Dan Amar zazzau. Sarautar Dan Amar ta sami asali ne a lokacin da wani yaro karami cikin 'ya'yan Sarkin Kano Usman ya ce ma mahaifinsa Sarkin kano, cewa sai an nada shi sarauta, ya hau doki kamar sauran 'yan uwansa,to daga nan ne aka nada shi Dan-Amir daga nan ta koma Kalmar Dan Amar, wani kaulin kuma ance Autansa ne Dan Amarya.
.
=== KIRARIN DAN-AMAR ===
AZURFA GA MAI RABO
SARFA GANDUN BAIWA
MALIYA BABBAR KOGI
MASU GARI DA GARINSU
DAN AMAR UBAN GABASAWA
Wannan shi ne kirarin Dan Amar da irin kasaitarwa.
.
59. SARKIN SHANUN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Sarkin Shanu, sarauta ce ta Fulani, kuma sarauta ce da ake ba mutum don mahimmancinsa, ko kwazonsa kuma sarauta ce ta Hakimci. An fara yin ta a zamanin Sarkin Zazzau Muhammadu Sani. Wanda aka fara nadawa wannan sarauta shi ne Malam Ibrahim Sarkin Shanu jikan Magajin Doko, dan Yamusa Sarkin zazzau.
.
=== KIRARIN SARKIN SHANU ===
SARKIN SHANUN SARKI
MAI KOGIN MADARA
MAI KOGIN NONO
Wannan shi ne kirarin Sarkin Shanu da irin daukakar mulkinsa.
.
60. DAN MAKWAYON ZAZZAU
Wannan sarauta ta Danmakwayo tana cikin sarautun da aka aro cikin wannan zamani na Mulkin Fulani kuma sarauta ce ta Hakimci a yanzu. An fara yin ta a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris. Wanda aka fara nadawa shi ne Mal. Muhammadu S. Magaji. Yana zaune a kaduna yama Hakimcin kawo.
.
=== KIRARIN DAN MAKWAYO ===
DAN MAKWAYON SARKI
DAN MAKWAYON DODO
DAN MAKWAYON UBAN GABASAWA.
.
61. MAGAJIN RAFIN ZAZZAU
Wannan Sarauta ta Magajin Rafi, tana daya daga cikin sarautu da aka aro cikin wannan zamani na Mulkin Fulani. Sarautar Magajin Rafi sarauta ce ta Hakimci a yanzu kuma an fara nada ta a zamanin sarkin zazzau Shehu Idris. Wanda aka fara nadawa shi ne Alh. Hari yakawada.
.
=== KIRARIN MAGAJIN RAFI ==
MAGAJIN RAFIN SARKI
MAGAJIN RAFIN DODO
MAGAJIN RAFIN UBAN GABASAWA
.
62. DAN KADEN ZAZZAU
Sarautar Dan kaden Zazzau Tana daya daga cikin Sarautun da aka aro a cikin wannan zamani na Mulkin daular Fulani. Wannan sarauta kuma tana cikin Sarautar Hakimci. An fara nada ta a lokacin Mulkin Sarkin zazzau Shehu Idris. Wanda ya fara wannan sarauta shi ne Alh. Ja'afaru Mohammed, Kaduna.
.
=== KIRARIN DAN KADE ===
DAN KADEN SARKI
DAN KADEN DODO
DAN KADEN UBBAN GABASAWA
.
63. BANAGAN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Banaga tana cikin sarautun Habe na asali. Wanda sarautana da ma'ana. Mai fitar da Hanyar da za a ratsa kogi ko kuma fitar da hanyar bin sarki zuwa wata kasa, don kauce wa abokan gaba. Kuma yana Hadiman Sarki, a wancan lokaci na Mulkin Habe. Wannan sarauta ta sami daukaka a wannan zamani na Mulkin Fulani ta kasance sarautar Hakimci kuma ana ba muhimmin mutum ne a kasa. Wanda aka fara nadawa a matsayin Hakimi shi ne Alh. Armaya'u Sulaiman daga gidan Gidadawan zazzau.
.
=== KIRARIN BANAGA ===
BANAGAN SARKI
HANA DORINA MATSO
JIRGIN FITON SARKI
SA TSINTSIYA SHARE DAWA
BANAGAN UBAN GABASAWA.
.
64. SHETTIMAN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Shettiman zazzau tana daya daga cikin sarautun da aka aro a zamanin Mulkin Sarkin zazzau Alh. Shehu Idris, kuma sarauta ce ta Hakimci babba. Wanda aka fara nadawa shi ne Mal. Abdullahi Nalado kaya.
.
=== KIRARIN SHETTIMA ===
SHETTIMAN SARKI
SHETTIMAN DODO
SHETTIMAN UBAN GABASAWA
.
65. ZANNAN ZAZZAU
Wannan sarauta ta zannan zazzau an aro ta ne a wannan zamani na Mulkin fulani a karkashin Mulkin Sarkin zazzau Alh. Shehu Idris. Kuma sarauta ce ta Hakimci da ake ba muhimman mutane. Wanda ya fara wannan sarauta shi ne Alh. Sa'idu Muhammed, Hakimin Tudun wadan Kaduna.
.
=== KIRARIN ZANNA ===
ZANNAN SARKI
ZANNAN DODO
ZANNAN UBAN GABASAWA
.
66. MABUDIN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Mabudin zazzau tana daya daga cikin sarautu da aka aro a cikin zamanin Mulkin Fulani. Kuma sarauta ce ta Hakimci yanzu a kasar zazzau. Wanda ya fara wannan sarauta shi ne Mal. Nuhu Bature daga kudancin Zariya (Agwan Bajju). Bayan raba yankunan mulki sai aka nada Malam Hussaini Alhassan, na zariya, a matsayin Mabudin Zazzau.
.
=== KIRARIN MABUDI ===
MABUDIN SARKI
MABUDIN DODO
MABUDIN UBAN GABASAWA
0 Comments