TSARIN HAKIMAI DA AIKINSU DA KIRARINSU
.
KASHI NA SHA HUDU (14)
.
83. BARAYAN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Baraya sarauta ce ta Habe kuma tana daya daga cikin sarautun Yaran Sarki masu masa hidima. Wannan sarauta ta daukaka a wannan zamani na Mulkin Fulani inda ta koma sarautar Hakimci yanzu. Wanda ya fara yin wannan sarauta a matsayin Hakimci shi ne Alh. Umar Bello Meyere.
.
Yanyu akwai Baraya guda biyu, Barayan Sarki daya daga cikin Hadiman Sarkin zazzau na fada, akwai kuma barayan zazzau, Hakimin Sarki.
.
=== KIRARIN BARAYA ===
GAIKAU BARAYAN SARKI,
GAIKAU BARAYAN DODO
TAFI DA GASKIYA KA DAWO DA AMANA.
.
84. YARIN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Yarin zazzau sarauta ce ta Habe wadda fulani suka gada. Wannan sarauta ce mai kula da gidan wakafi (kurkuku) kuma sarauta ce babba a karkashin Sarki. Kuma tana cikin sarautun da ake ba 'ya'yan Sarki a Mulkin daular Fulani a kasar zazzau. Wannan sarauta ta Yari ba a sami wanda ya fara yin ta ba saboda sarauta ce a karkashin Sarki, a cikin gida.
.
=== KIRARIN YARI ===
MANDAWARIN FARIN KARFE
SANKARA BABBAR LAYA
MAGANIN BARAWON ZAUNE
YARIN SARKI
.
85. SARKIN ZANAN ZAZZAU
Wannan sarauta tana daya daga cikin sarautun Habe na asali da Fulani suka gada. Ma'anar wannan sarauta, ta sarkin zana a lokacin Habe, ita ce Manzon sarki tsakaninsa da Matan Fada. Kuma shi ne Alhakin Tarbiyyar matan Fada ke hannunsa tare da tarbiyan 'ya'yan Sarki da yin musu hukunci in sun yi laifi. Yanzu daular Fulani ta daukaka wannan sarauta ta zama ta Hakimci. Wannan sarauta wanda ya fara yin ta shi ne Amshe, bayan tsawon lokacim Mulkin Habe. An nada wannan sarauta a lokacin Mulkin Sarkin zazzau Malam Yero. Wanda aka fara nadawa shi ne sarkin zana Muhammadu na Unguwan Bishar.
.
=== KIRARIN SARKIN ZANA ===
SARKIN ZANAN SARKI
SARKIN ZANAN DODO
SARKIN ZANAN UBAN GABASAWA
.
86. SARKIN TSABTAR ZAZZAU
Wannan sarauta ta sarkin Tsbta sarauta ce wadd fulani suka kirkire ta a wannan zamani nasu. Sarkin Tsabta shi ne yake kula da tsabtace Gari, da lafiyar Jama'a. Yanzu wannan sarauta ta sami daukaka ta koma sarautar Hakimci. Wanda ya fara wannan sarauta shi ne Malam Muhammadu Aminu Sarkin zazzau. Kafin ya yi sarautar Iyan zazzau a lokacin da aka raba sarautun mukamai na ma'aikatun En'e (N.A).
.
=== KIRARIN SARKIN TSABTA ===
SARKIN TSABTAN SARKI
MARA TSABTA YA GUJE KA
MAI TSAFTA YA JI DADI.
.
87. MARADIN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Mardadin zazzau tana daya daga cikin sarauvn da aka aro a cikin wannan zamani na Mulkin daular Fulani a zazzau kuma sarauta ce ta Hakimci. An fara nada ta a zamanin Sarkin Zazzau Shehu Idris. Wanda ya fara yin wannan sarauta shi ne Alh. Haruna Muhanad Jumare.
.
=== KIRARIN MARADI ===
MARADIN SARKI
MARADIN DODO
MARADIN UBAN GABASAWA.
.
89. DANEJIN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Danejin Zazzau, tana daya daga cikin sarautun da aka aro aka nada ta a wannan zamani na Mulkin daular Fulani. An fara nada ta a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris. Wanda ya fara wannan sarauta shi ne Alh. Isah Abdullahi Soba.
.
=== KIRARIN DANEJIN ZAZZAU ===
DANEJIN SARKI
DANEJIN DODO
DANEJIN UBAN GABASAWA
.
90. TUKURAN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Tukuran zazzau, sarauta ce ta Habe wadda aka daukaka ta a wannan lokaci na Mulkin Fulani domin yanzu sarauta ce ta Hakimci a masarautar Zazzau. Wanda ya fara wannan sarauta shi ne Malam Mahmuda Adamu, Hakimin Hunkuyi.
.
=== KIRARIN TUKURA ===
TUKURAN SARKI
TUKURAN DODO
TUKURAN UBAN DODO
.
91. SARKIN SHARIFAN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Sarkin Sharifai sarava ce wadda Fulani suka kirkire ta suka karrama ta kuma sarauta ce da ake ba malami mai ilimi, a matsayin sarautar Hakimci mai kula da sharifai na Gida da baki. An fara nada ta a zamanin Sarkin Zazzau Shehu idris. Wanda ya fara wannan sarauta shi ne, Alh. Isah Kwangero.
.
=== KIRARIN SARKIN SHARIFAI ===
SARKIN SHARIFAN SARKI
SARKIN SHARIFAN DODO
SARKIN SHARIFAN UBAN GABASAWA
.
92. SARKIN KOFAR ZAZZAU
Wannan sarauta ta Sarkin Kofa tana daya daga cikin sarautu masu asali tun daga lokacin Mulkin Habe har zuwa yau lokacin fulani. Sarkin kofa, shi ne ke kula da kofofin shiga Gari da kula da shige da ficen jama'ar Gari. Wannan sarauta ba ta da sunan wanda ya fara yin ta a lokacin Mulkin Fulani saboda kowace kofa tana da Sarkinta a lokacin.
.
=== KIRARIN SARKIN KOFA ===
SARKIN KOFAR SARKI
SARKIN KOFAR DODO
SARKIN KOFAR UBAN GABASAWA
.
93. DAN GALADIMAN WAZIRI
Wannan sarauta ta Dan Galadiman Waziri sarauta ce da ta samo asali daga Sakkwato, tun bayan Jihadi. Wannan sarauta ta Dan Galadiman waziri, sarauta ce da ke karkashin waziri, amma kuma sarauta ce ta Hakimci a yanzu a kasar zazzau. Wannan sarauta ba ta da sunan wanda ya fara ta saboda sarauta ce a karkashin waziri.
.
=== KIRARIN DAN GALADIMAN WAZIRI ===
DAN GALADIMAN BABBAN GWADABE
NAMARDI GAMI DA WAZIRIN SARKI
KOGIN SHUNI NAMARDI.
0 Comments