BAYANI KAN TSOFAFFIN SARAUTUN HABE DA FULANI SUKA DAUKAKA MATSAYINSU A ZAZZAU

BAYANI KAN TSOFAFFIN SARAUTUN HABE DA FULANI SUKA DAUKAKA MATSAYINSU A ZAZZAU
.
Wadannan sarautu an nuna matsayinsu da asalinsu lokacin mulkin Habe da kuma matsayinsu yanzu a lokacin Mulkin Fulani. Ma'ana, an yi bayanin irin matsayinsu ne kawai a tsarin mulki na Habe da Fulani na masarautar zazzau wanda ya bambanta da wasu masarautu, kowa da irin tsariknsu da kuma sarautunsu. Haka kuma akwai bambancin tsarin aiki na wadannan sarautu a yau inda a wasu kasashe za a ga cewa wadansu daga cikin irin wadannan sarautu suna matsayin sarautun 'ya'yan Sarki wasu kuma suna matsayin sarautun da ba na 'ya'yan Sarki ba, ko kuma sarautu ne na yaran Sarki.
.
Akwai abin lura a nan game da tsarin wadannan sarautu kamar sarautar Majidadi, da Majidadin Sarki, kamar Barayi Hakimi da Barayan Sarki, kamar Kilishi Hakimci da na yaran Sarki. Wadannan sarautu akwai na Hakimci da na yaran Sarki. Ma'ana, wanda aka kira sunan sarautar aka ce na zazzau to, wannan yana matsayin Hakimci da na yaran Sarki. Ma'ana, wanda aka kira sunan Sarautarsa aka ce na zazzau to, wannan yana matsayin Hakimi ne a kasar zazzau kamar Madauchin zazzau, Hakimi, shi kuma Madauci cikin Gida, Madaucin Sarki. Irin wadannan sarautu suna da rikitarwa sai an kiyaye da yadda tsarin yake. Haka ma Barde da Barade inda kalmomin suka so su yi kama da juna, amma akwai bambancin ma'ana. Barde, shi ne asalin sarautar, Barade kuwa kalma ce da ta kunshi yawan jarumai. Barade an aro ne daga sa5wato, kuma sarauta ce mai zaman kanta, ta 'ya'yan Sarki, Kuma daga can aka kawo ta Zazzau.
.
Wadannan sarautu na kasa da aka ciro su ne  Sarautun Habe, wanda a yanzu Mulkin daular Fulani ta sake dauko su daga cikin kundin sarautun karkashin masarautar zazzau, tanada wadannan sarautu ta daukaka darajarsu zuwa hakimci a karkashin Mulkin Sarkin Zazzau Alh. Shehu Idris, sakamakon karin masarautu da Gundumomi da gwamnatin Jahar Kaduna ta yi, karkashin jagorancin Gwamnan Kaduna na Farar Hula, Ahmad Muhammad Makarfi. Wannan tsari ya sa aka dauko wadannan sarautu na Habe da fulani suka gada aka fara amfani da su a wannan masarauta ta zazzau a yanzu.  Wadannan sarautu matsayinsu ya bambanta a tsakanin aikinsu a Mulkin Habe a yanzu. An daukaka matsayin aikinsu a Mulkin habe da yanzu. An daukaka matsayin wadannan sarautu zuwa matsayin Hakimci cikin wadannan zamani na Mulkin Fulani.
.
Kowace sarauta da irin aikinta da matsayinta a wancan lokuntana Habe da kuma lokacin Mulkin Fulani a yanzu:-
.
1. MAHARIN ZAZZAU:- Shi ne mai Gyaran rauni idan ya faru a lokacin Habbe, amma yanzu hakimi ne a Daular Fulani. Wannan aiki an yi shi ne a lokacin Mulkin daular Habe. Wanda aka fara wannan sarauta a Mulkin Fulani shi ne Raphel Mash ( Hakimin Kamantan )
.
2. KWARMAZAN ZAZZAU:- Yana cikin manyan sansanai na Madaki a lokacin Habe, amma yanzu Hakimi ne na Daular Fulani. Wanda ya fara wannan sarauta ta Kwaremaza shi ne Mal. Sa'idu Inuwa.
.
3. BAUSHEN ZAZZAU:- Shi ne likitan Sarki idan wata lalura ta samu a gida ko a waje na rashim lafiya, lokacin Habe, �
.
Amma yanzu Hakimi ne a Mulkin Fulani. Wanda aka fara nadawa shi ne Alh. Aminu Musa, Hakimin Kaya.
.
4. KAIGAMAN ZAZZAU:- Yana cikin yaran Magajin Malam shi da Bakon Borno a lokacin Habe, amma yanzu Hakimi ne a wannan lokaci na Mulkin Fulani. Wanda aka fara nadawa shi ne Alh. Umaru Muhammed, zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris, kuma shi ne Hakimin Kidandan.
.
5. MAI DALAN ZAZZAU:- Yana daya daga cikin sarautun yaran Sarki a lokacin Habe amma yanzu Sarauta ce ta Fulani ta Hakimci. Wanda aka fara nadawa shi ne Alh. S. M Ibrahim. Kuma shi ne hakimin Danmahawayi.
.
6. WAGUN ZAZZAU :- Yana kula da kayan yakin Sarki, kuma shi ke dauke da wagon yaki sannan kuma mataimaki ne na Makama a kan rabon ganimar yaki a lokacin Habe amma yanzu sarauta ce ta Hakimci a wannan Daula ta Fulani. Wanda aka fara nadawa shi ne, Alh. Namadi Haruna, a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris, Kuma shi ne Hakimin Kauran Wali.
.
7. SHENAGUN ZAZZAU:- Shi ma mataimaki ne na Makama, amma aikinsa shi ne ya rika kula da kayan Dokin Sarki. Wanda aka fara nadawa shi ne Alh. Usman Ibrahim Doka, a zamanin Sarkin Zazzau Shehu Idris, Kuma shi ne Hakimin Doka.
.
8. MAGAJIN DANGI:- Yana kula da ma'amala tsakanin 'ya'yan Sarki ta bagaren maza da mata a lokacin Mulkin Habe, kuma sarautarsa ce ta Koma Magajin Gari, yanzu a cikin Mulkin Fulani kuma sarauta ce ta Hakimci. Wanda aka fara nadawa shi ne Alh. Muhammadu Mustapha, a zamanin Sarkin zazzau Shehu, kuma shi ne Hakimin Gubuci.
.
9. SULUKIN ZAZZAU:- Yana daga cikin yaran Sarki Masu yi ma Sarki Hidima. A yanzu cikin Mulkin Fulan sarauta ce ta Hakimci. Wanda aka fara nadawa shi ne Alh. Muhammadu Bawa, Hakimin Kufena.
.
10. GWABAREN ZAZZAU:- Aikin Sarautar Gwabare shi ne ya kunna fitilu, ya sa a shigifofin da Sarki ke zama domin Sallar Asham, a dukkan watan Azumi. A lokacin Mulkin Fulani sarauta ce ta Hakimci a zazzau. Wanda aka fara nadawa shi ne Alh. Aliyu Abubakar a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris, kuma shi ne Hakimin Gadas.
.
=== KARIN BAYANI ===
Yawancin wadannan sarautu da za a ka fada yanzu sarautu ne na Hadiman Sarkin zazzau a wancan Lokacin na mulkin Habe, kuma kowace sarauta tana da ma'anarta a matsayin aiki, amma wasu daga cikin sarautun ne na Hadiman masu manyan Mukamai.
.
Zamu ci gaba

Post a Comment

0 Comments