BAYANI KAN TSOFAFFIN SARAUTUN HABE DA FULANI SUKA DAUKAKA MATSAYINSU A ZAZZAU
.
KASHI NA BIYU (2)
.
11. KANGIWAN ZAZZAU:- Wannan sarauta ta Kangiwa aikinsa shi ne ya tattara dukkan naman da mafarauta suka kawo ya kai ma Sarki a lokacin Habe, amma yanzu sarauta ce ta Hakimci a zamanin Fulani. Wanda aka fara nadawa shi ne Alh. Umaru Haruna, Hakimin Kargi.
.
12. DURUMIN ZAZZAU:- Wannan sarauta ta Durumi aikinsa shi ne ya gyara wurin zaman Sarki a wurin yaki a lokacin Habe, amma yanzu sarauta ce ta Hakimci lokacin Mulkin Fulani. Wanda aka fara nadawa shi ne Alh. Hussaini Yusuf, Hakimin Rahama, alokacin Mulkin Sarkin Zazzau Shehu Idris bayan rasuwarsa aka nada Alh. Bello Lawal.
.
13. MAGAJIN NAGABAN ZAZZAU:- Wannan sarauta ta Magajin Nagaba tana daya daga cikin sarautun manyan yaran sarki a lokacin Mulkin habe, amma yanzu sarauta ce ta Hakimci a kasar zazzau karkashin Mulkin Fulani. Wanda aka fara nadawa shine Mal. Jumare Jalalu zariya, Hakimin Sabon Birnin Daji, a zamanin Sarkin Zazzau Shehu Idris bayan rasuwarsa aka nada dansa Mal. Abdullahi Jumare Jalalu.
.
14. BAROKAN ZAZZAU:- Wannan Sarauta ta Barokan Zazzau sarauta ce ta mata a lokacin mulkin Habe kuma ita ce babbar Jakadiyar Sarki a tsakaninsa da Sauran matan gida, amma yanzu sarauta ce ta maza kuma ta Hakimci a karkashin Fulani a zazzau. Wanda aka fara nadawa shi ne Alh. Salihu Abdullahi, Hakimin Kerawa. An nada shi a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris.
.
15. RUBUN ZAZZAU:- Wannan sarauta ta Rubu tana cikin sarautun yaran Sarki, kuma shi ke kula da kayan hatsi na gonar Sarki kuma duk kayan abinci na hannunsa a wancan lokaci na Habe, amma a lokacin mulkin Fulani rubu shi ne mai ajiye kayayyaki da a ke kaiwa sakkwato don gaisuwa da sarakuna ke kaiwa, kuma shi ne ke kai kayan zuwa ga Sarkin Musulmi, yanzu sarauta ce ta Hakimci. Wanda aka fara nadawa shi ne Mal. T Shu'aibu, Hakimin Garin Kurama, a lokacin Mulkin Sarkin zazzau Shehu Idris.
.
16. CINCINAN ZAZZAU:- Aikinsa shi ne sa ido kuma ya ji ko akwai wani hari na yaki da za a kawo ko ya samo labarin halin da kasa ke ciki sai ya sanar da sarki a wancan lokaci na Habe. Amma yanzu a cikin daular Mulkin Fulani sarauta ce ta Hakimci. Wanda aka fara nadawa shi ne Alh. D Muhammed. Hakimin Gimi. An nada shi a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris.
.
17. GAYAN ZAZZAU:- Sarautar Gayan tana daya daga cikin sarautun yaran sarki masu kula da shigowar baki cikin gari a wancan lokaci na Habe, amma yanzu cikin daular fulani sarauta ce a Hakimci. Wanda aka fara nadawa shi ne Alh. Musa Rufa'i Ikara, Hakimin Saulawa, an nada shi a zamanin Sarkin Zazzau Shehu Idris.
.
18. KILISHIN ZAZZAU:- Sarautar Kilishi tana sarautun yaran Sarki. Kilishi shi ke kula da mazauna da makwancin Sarki a wancan lokaci na Habe da yanzu ma lokacin Fulani. Sarautar Kilishin zazzau. Wanda aka fara nadawa kilishin zazzau shi ne Alh. Tanimu Shu'ibu Hakimin 'Yarkasuwa, an nadashi a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris.
.
19. SARKIN RAFIN ZAZZAU:- Sarkin Rafi shi ne ke kula da kogi da kuma masuntan ruwa da masu fito. A zamanin Habe, yana karkashin Mulkin Sarkin Ruwa, ana yanzu sarauta ce ta Hakimci. Wanda aka fara nadawa shi ne Alhaji Musa Haruna Hakimin Zuntu, an nada shi a zamanin Sarkin zazzau Shehu idris.
.
20. MADUGUN ZAZZAU:- Wannan sarauta tana daya daga cikin sarautun mayaka. Madugu shi ne ke jagorancin sakon Sarki a lokacin Habe, amma yanzu a zamanin Fulani sarauta ce ta Hakimci a zazzau. Wanda aka fara nadawa shi ne Alh. Musa Usman,Hakimin Dutsen wai. An nada shi a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris bayan rasuwarsa sai aka nada Mal. Mustafa Sani Gyallesu.
.
21. KUNKELIN ZAZZAU:- Sarautar Kunkeli Sarauta ce ta mayaka kuma shi ne Ke kula da mayakan Garkuwa a wancan lokaci na Mulkin Habe, amma yanzu Sarauta ce ta Hakimci a Mulkin Daular Fulani a zazzau. Wanda aka fara nadawa shi ne Alh Mustapha Bello Sani, Hakimin Kwaro. An nada shi a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris.
.
22. UBAN DAWAKIN ZAZZAU:- Sarautar Uban Dawaki na daya daga cikin sarautun yaran sarki kuma shi ke kula da abin da ya shafi bargar Sarki gaba daya. Wanda aka fara nadawa shi ne Mr David Kantiyok, Hakimin Madakiya. An nada shi a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris.
.
23. KACALLAN ZAZZAU:- Sarautar Kacalla, tana cikin sarautun yaran Sarki kuma shi ne Masinja ko Jakada Tsakanin Shehun Barno da Sarkin zazzau a wancan lokaci na Habe, amma yanzu sarauta ce ta Hakimci a wannan lokaci na fulani. Wanda aka fara nadaw shi ne Alh. Ya'u Isah, Hakimin Tudun wadan Kaduna. An nada shi a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris.
.
24. SARKIN MAI ZAZZAU:- Sarautar Sarki Mai tana cikin sarautun yaran Sarki a wancan lokaci na Habe, kuma sarava ce ta 'ya'yan Sarki har a lokacin Fulani, amma yanzu an karrama ta ta zama sarauta ta Hakimci a cikin wannan daula ta Mulkin Fulani a zazzau. Wanda aka fara nadaw shi ne Alh. Bala Ali, waziri Hakimin Gwaraji. An nada shi a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris.
.
25. BAJIMIN KUDUN ZAZZAU:- Bajimin kudu mataimakin Sarkin Kudu ne mai wakiltar Kudu a kan sha'anin mulki a wancan lokaci na Habe amma yanzu sarauta ce ta Hakimci a Mulkin Daular Fulani. Wanda aka fara nadaw shi ne Alh. Abdulrash3d, Hakimin Jaji. An nada shi a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris.
.
27. BARDEN KANKANAN ZAZZAU:- Barden Kankana yana daya daga cikin jaruman sansani na sarki. Idan Barde ya yi gaba wajen yaki, to Barden Kankana na tare da Sarki a wancan lokaci na Habe. A yanzu sarautar Barde sarauta ce ta Hakimci a wannan Daular ta fulani. Wanda aka fara nadaw shi ne Alh. Muhammad Dahiru Hakimin Pala. An nada shi a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris.
.
=== KARIN BAYANI ===
Wasu daga wadannan tsofaffin sarautu amma a yanzu sabbi an fara nada su ne a lokacin Mulkin Soja, lokacin Gwamnan Jahar Kaduna na Soja Kanar Lawal Ja'afaru Isa a cikin Shekarar 1991, lokacin da aka fara gundumomi a masarautar zazzau. Sarautu kamar Su-Jagaba da Baraya da Ubandawaki da Rubu da Dan Rimi na cikinsu.
.
Zamu cigaba
Kasar zazzau
0 Comments