BAYANI KAN TSOFAFFIN SARAUTUN HABE DA FULANI SUKA DAUKAKA MATSAYINSU A ZAZZAU (3)

BAYANI KAN TSOFAFFIN SARAUTUN HABE DA FULANI SUKA DAUKAKA MATSAYINSU A ZAZZAU
.
KASHI NA UKU (3)
.
28. MADAUCIN AREWA:- Madauci na daya daga cikin sarautun yaran sarki a lokacin Mulkin Habe, amma yanzu sarauta ce ta Hakimci a Mulkin Fulanin zazzau. Wanda aka fara nadawa shi ne Alh. Muhammadu zubairu, Hakimin Barnawa. An fara nada shi a zamanin Sarkin zazzau shehu Idris.
.
29. BARAYAN YAMMA:- Barayan Yamma shi ne ke kula da kofar Gabas na gidan Sarki kuma daya daga cikin yaran Sarki a wancan lokaci na Habe, amma yanzu sarauta ce ta Hakimci a karkashin Daular Fulani.  Wanda aka fara nadaw shi ne Alh. Yusuf Ibrahim Hakimin Makera. An nada shi a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris.
.
30. LIFIDIN ZAZZAU:- Lifidi, na daya daga cikin shugabanni na rundunar yaki na sarki mai kula da 'yan Lifidi, wanda mayaka ne na musammaan a wancan lokaci na Habe. Mayaka ne da ke kusa da Sarki suna sanye da hular fata da sulke a jikinsu kuma suna yaki ne domin kada a yi kusa da Sarki, watau domin kare Sarki. Yanzu Sarauta ce ta Hakimci a lokacin Fulani. Wanda aka fara nadawa shi ne Mal. Musa Yarima Hakimin Gwagwada.
.
32. JARMA:-  Jarma na daya daga cikin mayakan Sarki mai rikon sansani na yaki tare da sarki  a wancan lokaci na Habe. Yanzu sarava ce ta Hakimci a lokaci Daular Fulani a zazzau. Wanda aka fara nadawa shi ne Alh. Bello Yamusa, Hunkuyi.
.
32. JAGABA :- Wannan sarauta ta Jagaba tana daya daga cikin Sarautun Habe da Fulani suka gada kuma yana daya daga cikin Jaruman Mayaka a karkashin Rundunar Sarki. Yanzu wannan Sarauta ta Jagba sarauta ce ta Hakimci a kasar zazzau. Wanda aka fara nadawa shi ne Mr. Yohanna Hakimin Katugal.
.
33. GATAU:- Sarautar Gatau tana daya daga cikin Sarautun gaban sarki wanda ake yi ma yaran Sarki amintatu. Wannan sarauta ta Gatau sarauta ce ta Habe, amma yanzu sarauta ce ta Hakimci a Daular Fulani. Wanda aka fara nadawa shi ne Alh. Aliyu Abdullahi, Hakimin Turawa. An nada shi a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris.
.
34. KARFE :- Wannan Sarauta ta Karfe tana cikin sarautun Habe amma Fulani sun nada nasu shi ne Karfen dawaki. Wannan sarauta a yanzu sarauta ce ta Hakimci a karkashin Mulkin Fulani. Wannan sarauta an fara nada ta a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris.
.
35. CIRITAWA:-  Sarauta ce a cikin sarautun yaran sarki a lokacin Mulkin Habe. Wannan sarauta a yanzu sarauta ce ta Hakimci a karkashin Mulkin Fulani. Wanda aka fara nadawa Shi ne Alh. Yakubu Haladu, Kakimin Kudan, Wannan sarauta an fara nada ta a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris.
.
36. BIJIMIN GABAS : Wannan Sarauta ta Bijimin Gabas Tana daya daga cikin Sarautun Habe wanda Fulani suka gada. Kuma tana daya daga cikin sarautu masu asali. Wannan sarauta a yanzu sarauta ce ta Hakimci a karkashin Mulkin Fulani. Wanda aka fara nadawa Shi ne Alh. Habibu Suleman, Kakimin Kusallo, A nada sha a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris.�
.
37. BARWA:- Wannan sarauta ta Barwa tana cikin Sarautun Habe da Fulani suka gada kuma tana daya daga cikin sarautu manya na yaran Sarki. Barwa yana cikin shugabanni masu kula da wurin zaman Sarki. Kuma shi ne ke kula da masaukin Sarki a wurin yaki da duk wasu gyare-gyare a duk lokacin  da sarki ya tafi yaki zuwa wata kasa a wancan Mulki na Habe. Wannan sarauta a yanzu sarauta ce ta Hakimci a karkashin Mulkin Fulani. Wanda aka fara nadawa Shi ne Dr Chalif Dogo, Hakimin Unguwan Rimi.
.
38. MAGAJIN KWA :- Magajin Kwa shi ne shugaba mai kula da bayi masu ma'amalla a cikin Gida tare da kula da ayyukansu nayau da kullum da suke yi a cikin gidan Sarki a zamanin mulkin Habe.
.
39. BARDEN MAIDAKI:-  Shi ne ke kula da gina dakin Uwargidan Sarki tare da ayyukan da suka shafi bangaren matan Sarki a wancan lokaci na Habe, Wannan sarauta a yanzu sarauta ce ta Hakimci a karkashin Mulkin Fulani. Wanda aka fara nadawa Shi ne Alh. Umaru Muhammad daga gidan Sarautar Barebari, kuma yanzu sarauta ce ta 'ya'yan Sarki.
.
40. MADAUCIN KUDU :- Madauci yana daya daga cikin yaran Sarki mai kula da bayi masu kulawa da kayan Sarki na yaki ko ganima a kudu da kasa, kuma shi ke kula da shiga da fice na bangaren shiga da fita a sashen kudu inda yake wakilta.
.
41. HAUNI:- Shi ma Hauni yana daya daga cikin masu horo idan an sami laifi, sai a bashi izinin irin hukuncin da zai yi. Tana daya daga cikin sarautu mafi dadewa na yaran sarki. Amma yanzu an mayar da ita sarauta ta Hakimci a Karkashin daular Fulani.
.
42. KWARBBAI:- Wannan sarava tana daya daga cikin saravun mayakan Sarki a lokacin Habe, amma Wannan sarauta a yanzu sarauta ce ta Hakimci a karkashin Mulkin Fulani. Wanda aka fara nadawa Shi ne Mal. Muhammed Aliyu , Hakimin Haskiya.
.
Za mu ci gaba.
.
Gamasu bukatan cikakken wannan Littafi mai suna TARIHIN SARAUTU DA AL'ADU NA MASARAUTAR ZAZZAU zasu iya garzayawa kantin SANKORE EDUCATIOOAL PUBLISHERS LTD, wanda ke zangon Shanu Samaru Road, zaria , Kaduna state. Dan Karin bayani a tuntubesu ta wannan numbr 08036609871, 08034529095, 08035991957

Post a Comment

0 Comments