SARAUTUN MALAMAI

=== SARAUTUN MALAMAI  ===
Wadannan Sarautu ana nada su ne a gaban Sarki kamar yadda ake nada sauran Hakimai. Su ne kamar Haka:-
.
1. LIMAMIN JUMA'A ZAZZAU:- Limamin Juma'a a zazzau ya kasu kashi biyu watau Limamin juma'a wanda a yanzu shi ne Babban Limamin Zazzau shi ke ba da Sallar Juma'a a babban Masallacin zariya na kofar Fadar Mai Martaba Sarkin Zazzau. Akwai kuma Limamin Kona wanda shi ne ke bin Limamin Juma'a, kuma Shi ke ba da Sallah idan babu Limamin Gari. Limamin Juma'a na daya daga cikin masu zaben Sarki tun daga kafuwar Daular Usmaniyya a zazzau.
.
=== KIRARIN LIMAMIN JUMA'A ===
IMAMU NA ALLAH
IMAMU SHUGABAN SAHU
UBAN MAKARANTA.
.
2. LIMAMIN KONA NA ZAZZAU:- Wannan mukami na Limamin Kona, yana da dadadden Tarihi a zazzau jusan ma shi ne gidan farko da ake ba da karatu tun kafin zuwan Fulani kuma su suke ba da Sallah a wannan lokaci har ya zuwa yau. Limamin Kona na daya daga cikin 'Yan Majalisar Sarki kuma masu zaben Sarki Tun daga kafuwar Daular Usmaniyya a zazzau.
.
=== KIRARAN LIMAMIN KONA ===
IMAMU NA ALLAH
IMAMU SHUGABAN RAHU
MALAMI ABOKIN SARKI
UBAN MAKARANTA
.
3. NA'IBIN ZAZZAU:- Wannan sarauta tana'ibi sarauta ce wacce take karkashin Limamin Juma'a, shi ma yana ba da Sallah a lokacin da Babu Limamin Gari ko Limamin kona, Muddin ba sa nan shi zai ba da Sallah.
.
=== KIRARIN NA'IBI ===
MAI MAKARANTA
UBAN MAKARANTA
BA DA KARATU.
.
4. SARKIN LADANAN ZAZZAU:- Sarautar Sarkin Ladanai ita ma tana cikin rukunin wadannan Sarautu na Malamai kuma shi ne Ladanin Babban Masallacin Juma'a zazzau. Shi ma a na nada shi kamar yadda ake nada kowa daga cikin sauran malaman, a gaban Mai Martaba Sarkin Zazzau.
.
=== KIRARIN SARKIN LADANAI ===
MAI MAKARANTA
BA DA KARATU
ZAKARAN MA'AIKIN ALLAH
.
5. ALKALIN GARKAR ZAZZAU:- Wannan sarauta ta Alkalin Garkar zazzau tana daya daga cikin sarautu masu dadadden Tarihi a masarautar zazzau alkali ne wanda sarki ke nadawa kuma yana fada ne don gabatar da shari'u da shawarwarin abin da ya shafi hukunci a gaban Sarki kuma a wannan zamani yana cikin 'Yan Majalisar Sarki.
.
=== KIRARIN ALKALIN GARKAR ZAZZAU ===
KULIYA MANTA SABO
KULIYA MANTA SABO ABOKIN SARKI
KULIYA MANTA SABO ABOKIN DODO
ALKALIN GARKAN UBAN GABASAWA
.
6. SALANKEN ZAZZAU:- Salanke na daya daga cikin sarautun Malamai masu kula da sha'anin Addini da Shari'a a fada, yana daya daga cikin masu shari'a da kuma tantance Alkali kafin a nada shi alkalanci a lokacin mulkin Habe a zazzau.
.
7. MAGATAKARDAN ZAZZAU:- Magatakarda na daya daga cikin sarautun Malamai a fadar zazzau, kuma shi ne ke gabatar da karatu na karshen shekara da gudanar da binciken abubuwan da za su faru a sabuwar shekara. Sannan kuma shi Malami ne na Sarki na Musamman, shi ke rubutawa da ba da amsar takarda da aka yi ma Sarki a lokacin Mulkin Habe a zazzau.
.
8. MAGAJIN MALAM ZAZZAU: Sarautar magajin Malam na daya daga cikin sarautun Malamai a masarautar zazzau, a lokacin Mulkin Habe kuma shi ne wakilin Shehun Barno a lokacin da Barno ta shigo ta ci wasu kasashen Hausa da yaki�.
.
KARIN BAYANI:- AKWAI SAURAN SARAUTU WADANDA A WANCAN LOKACI MALAMAI AKE NADAWA KAMAR SARAUTAR WALI DAGA NAN SAI SALANKE DA MATAWALLE, AMMA A YANZU ANA IYA BA DA TA GA WADANDA BA MALAMAIBA.

Post a Comment

0 Comments