SARAUTUN WAKILAI MASU WAKILTAR SARKI A MA'AIKATU DA WURARE (1)

SARAUTUN WAKILAI MASU WAKILTAR SARKI A MA'AIKATU DA WURARE
.
KASHI NA FARKO (1)
.
Wadannan Hakimai Wakilai Sarautarsu ta samo asali ne daga sarautar Wakilan Sarki wadda ta kafu a karkashin Daular Mulkin Fulani. Wannan sarautu ta Wakilin Sarki shi ne akan tura idan an fitar da Hakimi ko ya mutu, ko ya tsufa, ya tafi ya rike wannan kasa kafin a yi shawarar wanda za a bi Hakimcin kasar. Sakamakon haka, wannan sarauta ta yi rassa zuwa wakilin Gabas da Wakilin Kudu da Wakilin Yamma da Wakilin Arewa, inda kowanne daga cikinsu ana iya tura shi wannan bangare na sarautarsa don ya kula da wannan yanki.
.
An kara samun sarautun wakilai a lokacin da turawa suka zo aka sami tsarin aiki na En'e (N'A) inda aka karkasa ma'aikatun Gwamnati kashi-kashi, kamar bangaren lafiya da Tsabta da Gona da Ilimi da Ayyuka da aikin Ma'aikata da Yaki da Jahilci da Gwandun Daji da Sauransu. Wannan ya sa aka nada wakilan Sarki a wadannan Ma'aikatu a tsarin Mulkin Fulani na zazzau tare da kasancewar duk wanda aka ba shi sarautar. Wasu kuma ana ba su irin wadannan sarautu saboda sun gada wurin iyayensu. Ga tsarin kamar Haka:-
.
1. WAKILIN GABAS ZAZZAU: Wakilin Gabas, shi ne ke kula da Gabashin zariya, karkashin ofishin Hakimin Birni da kewaye, a irin tsarin sarautar a da kafin a sami canje-canje a yanzu. Amma asalinta wakilin Sarkin zazzau ne a gabashin Garin zazzau idan bukatar wakilta din ta taso, kamar an sami rasuwar Hakimi ko an fitar da shi ko an dakatar da shi, ko za a tafi karbo albarkatun kasa duk wannan aikin wakilin Gabas ne. Haka kuma da wakilin Arewa da wakilin Yamma da Wakilin Kudu duk  Wadannan wakilai aikinsu iri daya ne. Amma yanzu bayan an sami tsarin aikace-aikace karkashin mulkin En'e (NA), Native Authority, Wakilai sun sami canjin aiki zuwa ofishin yanki na gundumar zariya da kewaye a karkashin ofishin masarautar zazzau da ke Fadar Zazzau. Wanda ke rike da wannan sarauta yanzu shi ne Dr Aliyu Kari.
.
2.  WAKILIN AREWA ZAZZAU:- Wakilin Arewa shi ne ke kula da Arewacin Garin zariya, karkashin ofishin Hakimin Birni da kewaye shi ma duk tsarin iri daya ne da na sarautar wakilai. Wanda ke rike da wannan sarauta yanzu Shi ne Alh. Sani Aminu.
.
3. WAKILIN KUDUN ZAZZAU:- Wakilin Kudu shi ne ke kula da Kudancin Garin Zariya a karkashin ofishin Hakimin Birni da kewaye kamar yadda sauran wakilai 'yan uwansa, ke kula da kowane bangaren da aka ba su. Wanda ke rike da wannan Sarava yanzu shi ne Alh. Muhammad Rabi'u Jafari.
.
4.  WAKILIN YAMMAN ZAZZAU:- Wakilin Yamma shi ne ke kula da Yammacin Zariya a karkashin Ofishin Hakimin Birni da Kewaya kamar Sauran wakilai. Wanda ke rike da wannan sarava yanzu shi ne Alh. Idris Abdullahi Hakimin Kakangi. Wadannan su ne Wakilan Sarki a Karkashin Ofishin Hakimin Birni da suke kamar matsayin Dagatai a cikin Garin Zariya. Masu Unguwanni suna karkashinsu ne saboda haka wadannan wakilai su ke aiki kamar na Dagatai. Wannan shi ne aikin wadannan Wakilai a ka'ida, kuma haka asalinsu yake. �

Amma yanzu akwai bambanci ba duka wanda ke rike da wannan sarauta ta Wakilci ke yin aikin ba, wasu suna rike da sarauta ne kawai amma ba tare da aikin ba.
.
5. WAKILIN BIRNIN ZAZZAU:- Yana karkashin Ofishin Birni ne, shi ne ke kula da aikace-aikacen ofishin Birni  abin da ya shafi tsare-tsaren aiki na ma'aikatan Birni kamar kasuwa da abin da ya shafi cikin Birni zazzau. Wanda ke rike da wannan sarauta yanzu shi ne Mal. Sa'idu Abubakar.
.
6. WAKILIN DOKAN ZAZZAU:- Shi ne ke kula da jami'an tsaro na 'Yan Doka har zuwa lokacin da aka mai da su 'Yan Sanda saboda a wancan lokaci 'Yan Doka da kurkuku duk suna karkashin Sarki ne. Kuma yana daya daga cikin sarautun da aka fara yin su ko aka kirkire su lokacin zuwan Turawan mulki don samun bayanai ingantattu a kan harkar tsaro. Wanda ke rike da wannan sarauta yanzu shi ne Alh. Ibrahin Dodo
.
7. WAKILIN OFIS ZAZZAU: Shi ne ke kula da tsare-tsaren aikin majalisar Sarki da daukan rahotanni da bayanan majalisa da kuma kula da tsarin aikin masarautar zazzau. Shi ne ke rike da Sakatare na En'e (N.A) Kamar sakataren Sarki. Wanda ke rike da wannan sarauta yanzu shi ne Alh. Aliyu Abdu Jirambo.
.
8. WAKILIN RAYA KASAR ZAZZAU:- Shi ne ke kula da duk abin da aka kawo don jin dadin Jama'a. Yana karkashin ofishin walwala da jindadin Jama'a na En'e. Kuma duk kusan wakilan bangarorin suna kawo masa rahoton aiki don ya gabatar wa hukuma. Ma'ana, wani rahoton aiki don ya gabatar wa hukuma. Ma'ana, wani rahoton aiki ko bukatuwa na ofishin ko na wani wakili ne yakan biyo ne ta Ofishin Wakilin Raya kasa. Wanda ke rike da wannan sarauta yanzu shi ne Alh. Aminu Yakubu Wanbai.
.
9. WAKILIN MAKARANTAR ZAZZAU:- Shi ne ke kula da makarantu da tsarin ilimin zamani, musanan abin da ya shafi gina makarantu a wuraren da ake bukata, da daukan Malamai a makarantu. Yana karkashin ofishin Ilimi na En'e kuma shi ne ke wakiltar Sarki a duk abin da ya taso game da ilimin zamani ko na Addini a masarautar zazzau. Wanda ke rike da wannan sarauta yanzu shi ne Farfesa Shafi'u Abdullahi.
.
10. WAKILIN SANA'A ZAZZAU:- Shi ne mai kula da sana'o'i na Maza da Mata, da kula da gina cibiyar koyar da Sa na'o'i kamar Saka da Dinki, da makamantansu. Shi ma ofishinsa na karkashin En'e (N.A). Wanda ke rike da wannan sarauta yanzu shi ne Alh. Lawal Atiku.
.
KARIN BAYANI
WADANNAN WAKILAI A WANCAN LOKACI SUNA RIKE DA MA'AIKATUN EN'E (N.A) A KARKASHIN OFISHIN SARKI, SABODA HAKA, SUNA MATSAYIN SHUWAGABANNI NE NA SASHE-SASHE, WASU KUMA SHUWAGABANNIN MA'AIKATU NE.
.
ZAMU CI GABA INSHAALLAHU

Post a Comment

0 Comments