SARKIN ZAZZAU DA MASU YI MASA HIDIMA


BABI NA GOMA SHA BAKWAI
SARKIN ZAZZAU DA MASU YI MASA HIDIMA
.
KASHI NA FARKO (1)
Sarki shi ne Mutum wanda aka zaba a matsayin shugaba na masarauta kuma shi ne duk wani nauyi na kula da kariya na Al-ummarsa suka rataya a wuyansa kamar abin da ya shafi adalci da da'a da zaman lafiya da addini da ka'idojin sharia. Kusan kowace kasa tana da irin wannan shugaba da ake kira sarki. A nan, kasar zazzau ce Masarautar gaba daya tat a hada da zariya da sauran gundumomin Mulki da ke karkashinta. Zariya da sauran gundumomin Mulki da ke karkashinta. Zariya kuwa ita ce yankin masarautan kawai. Wanda ke shugabancin wannan masarauta ta zazzau shi ne ake kira Sarkin zazzau, kuma shi ne ke nada Hakimai zuwa kowace gunduma don tafiyar da Mulkin kasarsa. Sarki yana da darajoji da ake kiransa da su kamar haka: Mai Girma Sarkin Zazzau, Mai Martaba Sarkin Zazzau. Haka ake girmama kowane Sarki a masarauta ta zazzau kafin a ambaci sunansa. Sarkin zazzau yana da tsare-tsare na Fadarsa kamar Haka: Hakimai 'yan Majalisar Sarki da Hakimai 'ya'yan Sarki da Hakimai masu Hakimcin Kasa da 'ya'yan Sarki da wadanda ba 'ya'yan Sarki ba. Yaran sarki na tare da shi kodayaushe. Hakimai 'yan Majalisa su ne masu ba sarki Shawara a kan duk wani abu da ya taso game da masarautar. Su kuma Hakimai masu kasa, su ne ke rike da gundumominsu, sai yaran Sarki su ne suke tare da Sarki suna yi masa aikace-aikacen mulki, kamar irin su Shantali da Shamaki da Kilishi da Baraya da Sarkin Dogarai da Sarkin zagi da sarkin Hawa da Majasirdi da Madaucin cikin Gida da Sarkin Hawa da kuma Sallama. Wadannan su ne yaran Sarki da suke tare da shi kowane lokaci kuma kowa da irin aikinsa a wajen sarki a tsarin Fada. Ga yadda abin yake:
.
SHANTALIN SARKIN ZAZZAU
Sarautar Shantali sarava ce wadda Fulani su ka gada wurin Habe, kuma sarauta ce babba wanda ake ba yaron Sarki ko Bawan Sarki. Kamar yadda wasu suka Sani Shantali na nufin Buta. Wannan sarava ta Shantali ta daukaka a lokacin Fulani har ma an taba nada wasu 'ya'yan Sarki wannan Sarauta a lokacin Mulkin Fulani a baya.
.
Shantali na tare da Sarki a kodayaushe ko a mota ko a gida ko a doki kuma yana daya daga cikin masu yi wa Hakimai ko Jama'ar gari iso wurin Sarki lokacin da aka zo wajen Sarki ko yin gaisuwar Fada.
.
=== KIRARIN SHANTALIN ZAZZAU ===
KAS KUYANGI BABBAN DARON SARKI
KAS KUYANGI BABBAN DARON DODO
DARO MAI SARKI
Wannan Shi ne kirarin Shantali, ana nuna matsayinsa a wajen Sarki.
.
SHAMAKIN SARKIN ZAZZAU
Shamaki na daya daga cikin manyan bayin Sarki. Wannan sarauta ta Shamaki tana daya daga cikin Sarautun Habe da Fulani suka gada, aka ci gaba da yin da ta. Shamaki ya kasance daga daya cikin masu kula da Bayi a lokacin daular Fulani kuma yana da Hakimai a Karkashinsa. Kuma an sami bambancin aiki a lokacin Mulkin Habe da na Fulani.
.
Shamaki na tare da Sarki a kowane lokacin fadanci da lokacin da Sarki ke bisa doki. Haka kuma shi ke yi ma Hakimai iso lokacim gaisuwar safe da zaman Majalisa bayan sun riga sun fito da Sarki daga cikin gida. Kuma shi   Ake bari tsaron gida lokacin da Sarki ba ya nan.
.
== KIRARIN SHAMAKIN ZAZZAU ==
KORAU KAN BAYI
DUKA DA TARNAKI
TABAIBAYI HANA TAFIYA
A GUDU MA BAWAN SARKI
KORAU MAI GORA
GORA UBANGIJIN BAYIN SARKI.
Wannan shi ne kirarin Shamaki. Ana nuna irin ikonsa da karfin mulkinsa a kan bayin Sarki.
.
MADAUCHIN CIKIN GIDAN SARKIN ZAZZAU
Wannan sarauta tana daya daga cikin sarautun da Fulani suka kirkira daga sarautar Madauci. Kuma shi ne shugcan duka bayin Sarki. Wannan sarauta tana da mahimmanci a cikin sarautun manyan yaran Sarki a wannan zamani na Mulkin Fulani. Yana tare da Saki  a kowane lokaci yana kofar dakin Sarki shi zai fito da Sarki tare da sauran fadawa zuwa waje. Sa6an yana daya daga cikin masu yin iso wajen Sarki, kuma shi ke ajiye kayan yaki na Sarki kamar takobi da mashin Sarki da sandar Girma da Tuta. Haka kuma idan Sarki ya rasu shi zai kwashe wadannan kayan sarauta ya ajiye a hannunsa, kuma idan an nada Sarki shi zai kawo wadannan kaya ya bayar a mika ma sabon Sarki.
.
== KIRARIN MADAUCHIN CIKIN GIDAN ZAZZAU ==
TSARA YA GAMU DA TSARA
MAGANIN GWAZA TOKA
MAGANIN KARARA SOSO
MADAUCHIN UBAN GABASAWA
Wannan shi ne kirarin Madauchin cikin Gida kamar yadda kirarin Madauchin Gari yake.
.
KILISHIN SARKIN ZAZZAU
.
Yana tare da sarki a kodayaushe, kuma shi ke kula da tsabtar dakin sarki da gyara wurin Kwanciya da wurin zaman Sarki a ko'ina da kula da Shimfidun Fada da masallaci da duk inda Sarki za shi ya zauna sai Kilishi ya tafi ya duba tsabta da mahimmanci da dacewar mazaunin Sarki.
.
BARAYAN SARKIN ZAZZAU
Baraya shi ne ke kula da bayin Sarki na cikin gida da zaben wanda za a yi kyauta da su. Yanzu Barayana cikin yaran Sarki wadanda koyaushe suke tare da shi. Aikin Baraya a Mulkin Fulani shi ne manzo tsakanin sarki da Rasdan ( Resident Officer ). Kuma shi ke yin gaba lokacin da Sarki ke rangadi ko ziyarar wani gari don tabbatar da wurin sauka mai kyau. Kuma shi ne ke karbar kayan aure na 'ya'yan Sarki kuma idan za'a aurad da 'yar Sarki shi zai kai ta gidan miji.
.
=== KIRARIN BARAYA ===
GAIKAU BARAYAN SARKI
GAIKAU BARAYAN DODO
TAFI DA GASKIYA KA DAWO DA HAKIKA
.
SARKIN DOGARAN SARKIN ZAZZAU
Wannan mukami na Sarkin Dogarai yana cikin mukamai na tsaro wanda aka fara shi tun wancan zamani na Mulkin Habe a zazzau. Kuma Fulani sun ci gaba da tafiyar da wannan matsayi na Sarkin Dogarai, kafin 'yan Doka. Dogarai ne masu tsaro da tabbatar da Doka da hukunci a kasa har zuwa lokacin Mulkin Fulani a yanzu.
.
Sarkin Dogarai shi ne shugcan tsaro na Sarki kuma shi kan sa a tafi don kamo mai laifi a duk lokacin da aka ba da umurni, a kodayaushe yana tare da Sarki don tsaro.
.
=== KIRARIN SARKIN DOGARAI ===
MAI SANDA DA MADIN KARFE
NA BAGARA DOGARIN SARKI
MAI TSABGA , MALA'IKAN 'YAN SARKI
SARKIN DOGARAN SARKI
.
SARKIN ZAGIN SARKIN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Sarkin Zagi an fara ta ne tun lokacin Mulkin Habe kuma Fulani suka ci gaba da ita. Sarkin Zagi shi ne mutum wanda ke gaban Sarki ko a ina yake don tabbatar da wurin ko gaban Sarki lafiya yake yana tafiya yana Tafiya yana ma sarki kirari a gabansa.
.
Yana tare da sarki, a duk lokacin da Sarki ke tafiya shi ke gcan Sarki kuma yana da yara a karkashinsa da ake ce ma zagage. Shi ma yana cikin cngaren tsaro. Kuma shi ne ke fada ma sarki cin da ke gabansa in suna tafiya da Sarki kamar in an zo kofa ko tudu ko gangare. Kuma kowane mutum wanda zai gaisuwa ga Sarki, Sarkin zagi zai fada ma sarki a cikin tafiya
.
=== KIRARIN SARKIN ZAGI ===
MAI SANDA DA KARIN KUNAMA
DARKAKAU UBAN NA KASA
DARKAKAU BAWAN SARKI

Post a Comment

1 Comments