TSARIN HAKIMAI DA AIKINSU DA KIRARINSU
.
KASHI NA SHA BIYU (12)
.
67. SARKIN MALAMAI
Wannan sarauta ta Sarkin Malamai tana daya daga cikin sarautun da Fulani suka kirkira lokacin da ba a yin amfani da sarautar Magajin Malam. Wannan sarauta ce ta Hakimci da ake ba mutum mai ilimi ko cikin 'ya'yan Sarki ko kowane mutum wanda ya shahara a kan aikin koyarwa. Wannan sarauta ta daukaka lokacin da aka kafa En,e (N.A) Shi ne shugaban dukkan malamai na masaravar zazzau karkashi Ene-e (Native Authority)
.
=== KIRARIN SARKIN MALAMAI ===
MAI MAKARANTA
UBAN MAKARANTA
BI DA KARATU AMANAN SARKI
SARKIN MALAMAN SARKI
DAN UBAN GABASAWA
.
68. SARKIN SUDAN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Sarkin sudan tana daya daga cikin sarautun da aka aro a wannan zamani na Mulkin Fulani cikin zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris. Kuma sarauta ce ta Hakimci mai girma a kasar zazzau. Wanda aka fara nadawa wannan sarauta shi ne Malam Abubakar Hayatu na Bambale.
.
=== KIRARIN SARKIN SUDAN ===
SARKIN SUDAN SARKI
SARKIN SUDAN DODO
SARKIN SUDAN UBAN GABASAWA
.
69. SARKIN BAI ZAZZAU
Wannan sarauta ta Sarkin bai tana daya daga cikin sarautu da aka aro a wannan lokaci na Mulkin Fulani a karkashin Mulkin sarkin zazzau Shehu idris. Kuma sarauta ce ta Hakimci mai girma. Wanda aka fara nadawa shi ne Alh. Falalu Bello, Dan Danmasanin zazzau Alh. Bello Sani Rigacikum
.
=== KIRARIN SARKIN BAI ===
SARKIN BAI SARKI
SARKIN BAI DODO
SARKIN BAI UBAN GABASAWA
.
70. DANMORIN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Danmori tana daya daga cikin sarautu da Fulani suka kirkiro a lokacin mulkinsu. Kuma sarauta ce ta kusa da Sarki wadda ake ba amintacce ko na jikin Sarki. Yanzu wannan sarauta ta Hakimci ce a karkashin Mulkin Fulani a zazzau. Wanda aka fara nadawa a matsayin Hakimi shi ne Malam Dogara iguda a matsayin Danmorin zazzau. Amma a da sarauta ce da take da sarauta na Hadiman Sarki.
.
=== KIRARIN DANMORI ===
DANMORIN SARKI
DANMORIN DODO
DANMORIN UBAN GABASAWA
.
71. 'YANDOTON ZAZZAU
Wannan sarauta ta 'Yandoto, tana daya daga cikin sarautun da aka aro a wannan zamani na mulkin Fulani karkashin Mulkin Sarkin zazzau Shehu Idris na ba da ita ga dan Sarki kowani muhimmin mutum a zazzau. Wanda aka fara nadawa wannan sarauta, shi ne, Alh. Sa'idu Aliyu na Unguwar Madaka.
.
=== KIRARIN 'YAN DOTO ===
'YANDOTON SARKI
'YANDOTON DODO
'YANDOTAN UBAN GABASAWA
.
72. DANRIMIN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Danrimi, tana daya daga cikin sarautun da aka aro a wannan zamani na Mulkin Fulani karkashin Mulkin Sarkin zazzau Shehu Idris, kuma sarauta ce ta Hakimci mai girman a kasar zazzau. Wanda aka fara nadawa wannan sarauta, shi ne, Alh. Muhammadu Garba.
.
=== KIRARIN DANRIMI ZAZZAU ===
DANRIMIN SARKI
DANRIMIN DODO
DANRIMIN UBAN GABASAWA
.
73. DOKAN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Doka tana cikin sarautun da aka yi su a zamanin Mulkin Habe, kuma sarauta ce mai kula da jami'an tsaro, da zartar da hukunci. Ana bayar da ita ga dan Sarki kowane muhimmin mutum a kasark zazzau. Daga baya an mayar da ita ta wakilin Doka lokacin Mulkin Turawan Mulkin Mallaka.
.
=== KIRARIN DOKA ===
DOKAN SARKI
DOKAN DODO
DOKAN UBAN GABASAWA
.
74. AJIYAN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Ajiya, Sarauta ce wadda ta samo asali daga sarautun Habe, kuma aikin Ajiya a wancan lokaci shi ne ya ajiye dukkan abin da aka samu na ganima ko abin da aka kawo ma sarki gaisuwa. Wannan sarauta ta daukaka zuwa sarautar Hakimci a lokacin Mulkin Fulani. Wanda ya fara wannan sarauta shi ne Alh. Sani Rimin Tsiya, a matsayin Hakimi cikin Zamanin Mai Martaba sarkin zazzau Alh. Shehu Idris
.
=== KIRARIN AJIYA ===
AJIYAN SARKI,
AJIYAN DODO
AJIYAN UBAN GABASAWA
.
75. GADO-DA-MASUN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Gado-da-masu, tana daya daga cikin sarautun da aka aro a cikin wannan zamani na Mulkin Fulanin Zazzau. Kuma sarauta ce ta Hakimci a yanzu. An fara nada ta a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris. Wanda ya fara yin wannan sarauta shi ne Alh. Musa Hassan.
.
=== KIRARIN GADO DA MASU ===
HAWANKA SAI GWANI
GADO DA MASUN SARKI
TSAYAR DA MAI GARAJE,
KA TSAYAR DA MAI NAWA
.
76. KAURAN ZAZZAU
Wannan sarauta ta kauran zazzau tana daya daga cikin sarautun da aka aro cikin wannan mulki na daular fulani a zazzau. Wannan sarauta ta kaura tana cikin sarautu na Hakimci a yanzu. Wanda ya fara wannan sarauta shi ne Alh. Ja'afaru Paki.
.
=== KIRARIN KAURA ====
MAI KUGEN AZURZA,
TARA SANSANI KA CI SU DA YAKI,
KAURAN SARKI
.
76. SARKIN GANDUN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Sarkin Gandu Tana daya daga cikin sarautun Habe da fulani suka karrama a ka ci gaba da yin ta har zuwa yau cikin Mulkin Fulani. Sarkin Gandu shi ne mai kula da filaye da rabo na sarki a ko'ina cikin yankin kasar Sarki. Wannan sarauta ta inganta zuwa sarautar Hakimci a yanzu. Wannan sarauta ba a sami hakikanin wanda ya fara yin ta ba, domin sarauta ce ta yaran sarki kafin a dankata ta zama ta Hakimci.
.
=== KIRARIN SARKIN GANDU ===
SARKIN GANDUN SARKI
SARKIN GANDUN DODO
SARKIN GANDUN UBAN GABASAWA
0 Comments