TSARIN HAKIMAI DA AIKINSU DA KIRARINSU (17)

TSARIN HAKIMAI DA AIKINSU DA KIRARINSU
.
KASHI NA SHA BAKWAI  (17)
.
112. UBAN GARIN ZAZZAU
Sarautar Uban Garin zazzau, sarauta ce wadda aka aro ta daga yankin Nasarawa, wanda aka fara nadawa wannan sarautar shi ne Alh. Bashir Shehu Idris, a cikin zamanin mulkin Sarkin zazzau Alh. Shehu Idris.
.
=== KIRARIN UBAN GARI ===
UBAN GARIN ZAZZAU
UBAN GARIN SARKI
DAN UBAN GABASAWA
.
113. GARKUWAR KUDU
Wannan sarauta ta Garkuwar Kudu an fara nada ta ne a zamanin Mulkin Fulani, wanda aka fara nadawa wannan sarauta shi ne Alh. Muhammadu Sani Uwaisu cikin mulkin Sarkin Zazzau, Alh. Shehu Idris.
.
=== KIRARIN GARKUWAR KUDU ===
KIRGI ADON MAZA
KIRGI SHA KAKKABA
GARKUWAR UBAN GABASAWA
.
114. FAGACIN DAWAKIN ZAZZAU
Wannan sarauta Fagacin Dawaki, tana daya daga cikin tsofaffin sarautu na zamanin mulkin Habe. An karrama ta a lokacin mulkin Fulani. A zamanin Sarkin zazzau Malam Yamusa ta koma sarautar 'ya'yan Sarki. Wanda ke rike da sarautar shi ne Ibrahim Sambo dan Walin Zazzau.
.
=== KIRARIN FAGACIN DAWAKI ===
BINA BABBAN DAKIN SARKI
DAKIN KASA DA KASA INDA GOBARA TA JI KUNYA
FAGACHIN DAWAKI UBAN GABASAWA
.
115. BARDEN YAMMAN ZAZZAU
Barden Yamma yana daya daga cikin Baraden Sarki mai kula da yammacin kasa duka a karkashin ikon Barde, a wancan lokaci na Mulkin Habe. Yanzu sarautar Barde sarauta ce ta Hakimci a wannan Daula ta Fulani. Wanda aka fara nadawa shi ne Alh. Yahuza Ishaq Danmahawayi, Hakimin Fatika. An nada shi a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris.
.
=== KIRARIN BARDE YAMMA ===
GOBARAR GASHIN GARI
GOBARAR KASHE ARNA
FASA GARI BA TUYA.
.
116. BARDEN GABAS
Barden Gabas yana daya daga cikin Dakarun Sarki wanda ke kula da gabas don jin labarin ko shirin kawo hari a kasa a wancan lokacin na Habe, amma yanzu sarauta ce ta Hakimci a Mulkin Fulani. Wanda aka fara nadawa shi ne Alh. Musa Rufa'i Ikara, Hakimin Saulawa. An nada shi a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris.
.
=== KIRARIN BARDEN GABAS ===
GOBARAR GASHIN GARI
GOBARAR KASHE ARNA
FASA GARI BA TUYA
.
117. BARDEN KUDU
Barden Kudu yana daga cikin Dakarun Sarki wanda ke kula da Kudanci don tsarewa ko jin labarin ko shirin kawo hari a kasa a wancan lokaci na Habe, amma yanzu sarauta ce ta Hakimci da ake ba 'yayan Sarki a Mulkin Fulani. Wanda aka fara nadawa shi ne Alh. Shehu Tijjani jikan Sarkin zazzau Alu dan Sidi Hakimin kakuri. An nada shi a zamanin Sarkin Shehu Idris.
.
=== KIRARIN BARDEN KUDU ===
GOBARAR GASHIN GARI
GOBARAR KASHE ARNA
FASA GARI BA TUYA TSAYAYYEN NAMIJI
DAN UBAN GABASAWA
.
118. TURAKIN DAWAKIN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Turakin Dawaki ita ma tana daya daga cikin saravu masu tsohon tarihi a zazzau. An fara nada ta a lokacin mulkin Habe, kuma an kara karrama ta ta koma zuwa sarautar 'ya'yan Sarkin a lokacin mulkin Fulani. Wanda ke rike da ita shi ne Alh. Ramalan yero.
.
=== KIRARIN TURAKIN DAWAKI ===
TURKE MADAURA GIWA
TURAKI TURAKAN SARKI
SURI MATATTARA KASA
FADANCIN MAJE DAKA ALLAH KA SO NA WAJE
.
�119. MARAFAN MALAMAN ZAZZAU
Sarautar Marafan Malamai na daya daga cikin sarautun da aka nada a lokacin mulkin Fulani cikin zamanin Sarkin zazzau Alh. Dr Shehu Idris kuma wanda aka fara nadawa wannan sarauta shi ne Dr. Dalhatu Muhammad.
.
=== KIRARIN MARAFAN MALAMAI ===
MARAFAN MALAMAN MALAMAI
MARAFAN MALAMAN SARKI
MARAFAN MALAMAN UBAN GABASAWA
.
120. BARADEN DAWAKI
Sarautar Baraden Dawaki na daya daga cikin sarautu da aka nada su a zamanin mulkin Fulani cikin zamanin mulkin Sarkin zazzau Alh. Dr. Shehu Idris, wanda aka fara nadawa wannan sarauta shi ne Alh. Umar Yakubu.
.
=== KIRARIN BARADEN DAWAKI ===
FASA GARI BA TUYA
GOBARAR GASHIN GARI
GOBARAR GASA ARNA
BARADEN DAWAKI UBAN GABASAWA
.
121. GARKUWAN DAWAKI
Wannan sarauta ta Garkuwar Dawaki tana daya daga cikin sarautu na Jaruman fada. Kuma sarava ce mai mahimmanci, an fara nada ta a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris kuma wanda aka fara nadawa shi ne Alh. Yusuf Tijjani.
.
=== KIRARIN GARKUWAR DAWAKI ===
KIRGI ADON MAZA
KIRGI SHA KAKKABA
GARKUWAN DAWAKI UBAN GABASAWA
.
122. GARKUWAR MALAMAN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Garkuwar Malamai an fara nada ta ne a cikin zamanin mulkin Fulani karkashin Mulkin Mai Martaba Sarkin Zazzau Shehu Idris kuma wanda aka fara nadawa wannan sarauta shi ne Malam Shitu Maloli.
.
=== KIRARIN GARKUWAR MALAMAI ===
KIRGI ADON MAZA
KIRGI SHA KAKKABA
GARKUWAR MALAMAI UBAN GABASAWA
.
123. GARKUWAR MANOMAN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Garkuwar Manoma an fara nada ta ne a cikin zamanin Mulkin Fulani karkashin Mulkin Mai Martaba Sarkin Zazzau Shehu idris, wanda aka fara nadawa wannan sarauta shi ne Alh. Sama'ila Haladu, Garkuwar Manoman zazzau wanda yake wakilci tsakanin gwamnati da manoma a kan abubuwan da suka shafi manoma da Fulani ko kan wata annoba da ta zo wa manoma a lokacin amfanin gona, kamar su: barnar tsuntsaye ko fari ko tsutsotsi, domin gwamnati ta magance abin.
.
=== KIRARIN GARKUWAR MANOMA ===
KIRGI ADON MAZA
KIRGI SHA KAKKABA
GARKUWAR MANOMA UBAN GABASAWA
.
124. MALLAMAWAN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Mallamawan zazzau sarauta ce wadda fulani suka gada wurin Habe daga baya aka dawo da ita a karkashin Sarkin Malamai. Wanda aka fara nadawa a cikin Mulkin Fulani shi ne Alh. Danjuma Adamu, cikin zamanin Mulkin Sarkin zazzau Shehu Idris.
.
=== KIRARIN MALLAMAWAN ZAZZAU ===
MALLAMAWAN SARKI
MALLAMAWAN DODO
MALLAMAWAN UBAN GABASAWA
.
125. MAKAMAN MALAMAN ZAZZAU
Sarautar Makaman Malamai, tana daya daga cikin sarautu da aka kirkire su a cikin Mulkin daular Fulani cikin zamanin Sarkin zazzau Alh. Shehu Idris. Wanda aka fara nadawa wannan sarauta shi ne Mal. Sani Yusuf Magaji daga gidan Torankawa na zazzau.
.
=== KIRARIN MAKAMAN MALAMAI ===
ABDALLAH MAKAMA GAMI DA MALAMAI
SHATARITA MAKAMA
ABDALLAH SA GARI GUDU
TOGAI RUMFAR SARKI

Post a Comment

0 Comments