TSARIN HAKIMAI DA AIKINSU DA KIRARINSU
.
KASHI NA SHA BIYAR (15)
.
94. FALAKIN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Falakin zazzau tana cikin sarautun da aka aro a wannan zamani na Mulkin Fulani. Sarautar Falaki tana daya daga cikin sarautun Hakimci a masarautar zazzau. An fara nada ta a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris. Wanda aka fara nadawa wannan sarauta shi ne Mal. Abba Ibrahim.
.
=== KIRARIN FALAKI ===
FALAKIN SARKI
FALAKIN DODO
FALAKIN UBAN GABASAWA
.
95. MADARAN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Madaran zazzau tana cikin saravun da aka gada na Habe wannan mulki na zamanin Fulani kuma sarauta ce ta Hakimci a wannan Masarauta. An fara nada ta a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris, kuma wanda aka nada shi ne Alh. Sani, sarkin Fada, Hakimin wucicciri
.
=== KIRARIN MADARA ===
MADARAR SARKI
MADARAR DODO
MADARAR UBAN GABASAWA
.
96. MAYANAN ZAZZAU
.
Wannan sarauta ta Mayana tana daya daga cikin sarautun da aka aro daga wasu masarautu a cikin wannan zamani na Daular Mulkin Fulani a zazzau. Kuma sarauta ce ta Hakimci, an kuma fara nada ta a zamanin Sarkin zazzau Shehu Idris. Wanda aka fara nadawa wannan sarauta shi ne Malam shehu Aliyu, a lokacin Mulkin Sarkin zazzau Shehu idris.
.
=== KIRARIN MAYANA ===
MAYANAN SARKI
MAYANAN DODO
MAYANAN UBAN GABASAWA
.
97. GALADIMAN DAWAKIN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Galadiman Dawaki na daya dag cikin sarautu da aka gada wurin Habe. Wannan sarauta an draja ta lokacin Mulkin Fulani a kasar zazzau kuma sarauta ce ta Hakimci a wannan masarauta. Wannan sarauta ta Galadiman Dawaki an fara nada ta a kan Alh. Abubakar Mohammed, jikan sa'in zazzau Mazadu.
.
=== KIRARIN GALADIMAN DAWAKIN ZAZZAU ===
NAMURDO KOGIN SHUNI
DAURU RANA DA HAZO
GALADIMAN DAWAKIN SARKI
.
98. SARKIN FULANIN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Sarkin Fulanin zazzau, sarauta ce da Fulani suka kirkire ta suka kuma daraja ta. Kuma sarauta ce da take kula da al'amuran da suka shafi Fulani mazauna da baki. Yanzu sarautar ta zama ta Hakimci. Wanda aka fara nadawa wannan sarauta a matsayin Hakimi,, shi ne, Alh. Barau Aliyu Damau, Sarkin Fulanin zazzau.
.
=== KIRARIN SARKIN FULANI ===
TURKE DA MAI KAHO
MAI KOGIN NONO
FULANI MAI SARKI
SARKIN FULANIN SARKI
.
99. SARKIN YARAN ZAZZAU
Sarautar Sarkin Yara, tana daya daga cikin sarautun da fulani suka gada wurin Habe. Wannan sarauta ta Sarkin yara sarava ce da ake ba Jikan Sarki a wannan lokacin na Habe. Amma yanzu lokacin Mulkin fulani an mayar da ita sarautar 'ya'yan Sarki ko kowane muhimmim mutum cikin kasa. Wanda ya fara wannan sarauta, shi ne, Da shara dan Yamusa na Gidan barebari.
.
=== KIRARIN SARKIN YARA ===
ADO DA KATTI GOMA
TAFIYA DA GAMZAME
SARKIN YARAN SARKI
SARKIN YARAN DODO
DAN UBAN GABASAWA
.
100. SARKIN AYYUKKA
Sarautar Sarkin Ayyukka na daya daga cikin saratun da fulani suka kirkira a wannan zamani na Mulkin fulani kuma shi jami'i ne a karkashin ofishin ayyuka na Hukuma, mai kula da aikace-aikace hanyoyi da gyare-gyaren Fada da ma'aikatu a wancan lokaci. Wanda ya fara wannan sarauta shi ne Fagachi Muhammadu, kafin ya yi sarautar Fagachi, a zamanin Sarkin zazzau Ibrahim Dan Kwasau. Wanda ke rike da sarautar yanzu shi ne, Malam Abbas Mohammed Fagachi dan Fagachi Muhammadu.
.
101. KUFENAN ZAZZAU
Wannan sarauta ta Kufenan zazzau tana daya daga cikin sarautun Habe. Wannan sarauta ta Kufena sarauta ce wadda take kula da mazaunan Habe na farko a ganuwar zariya, amma yanzu cikin daular Fulani sarauta ce ta Hakimci.
.
102. MAINAN ZAZZAU
Sarautar Maina an aro ta ne daga cikin sarautun Borno. Wannan sarauta ta Maina sarauta ce da ake kiran duk wani Dan Shehun Borno, kamar yadda saravar Yarima ta daukaka duk wani wanda za a ce shi Dan Sarki ne. Ma'ana, Yarima dan sarki. Wannan sarauta an fara nada ta a kan Dr Muhammad Sani Bello, zamanin mulkin Sarkin zazzau Alh. Shehu Idris.
.
=== KIRARIN MAINA ===
MAINAN SARKI
MAINAN DODO
MAINAN UBAN GABASAWA
.
103. CIGARIN ZAZZAU
Wannan sarava ta Cigari an aro ta ne daga Kano a cikin wannan mulki na Fulani, zamanin mai Martaba Sarkin zazzau Shehu Idris. Wanda aka fara nadawa wannan sarauta shi ne Alh. Shehu Ladan, dan Dan Iyan zazzau Mal. Muhanadu Ladan.
.
=== KIARARIN CIGARI ===
CIGARIN SARKI
CIGARIN DODO
CIGARIN UBAN GABASAWA
0 Comments