WAMBAN ZAZZAU
Sarautar Wambai, a lokacin Habe, sarauta ce wadda ba ta da wani matsayi kuma aikinsa a wancan zamani shi ne yake tattara mvanen da suka nakasa a wajentyaki ya kawo su gari. Shi ke kula da wurin ajiye gajiyayyu da tsabtace cikin gidan Sarki. Kuma shi ne ke gabatar da sha'anin aure ko suna a fada. Sarautar Wambai, karkashin Daular Fulani, sarauta ce wadda ake ba Dan Sarki wanda ya gaji sarautar sarki. Kuma tana daya daga cikin sarautu masu daraja a cikin sarautun da ake ba 'ya'yan sarki na cikin Hakiman Gunduma. Saboda haka, wannan sarava ta wambai ta sami canji da matsayi a zamanin Mulkin daular Fulani. Wanda ya fara wannan sarauta ta wambai a karkashin Mulkin Fulani, shi ne wambai Doko Marwa dan Sarkin zazzau Malam Yamusa, cyan an karba daga hannun Habe.
.
=== KIRARIN WAMBAI ===
WAMBAN SARKI
WAMBAI GIYE DA GARI,
WAMBAI GIYE DA KASA,
TAITAYA GURAGU AMALE,
DAN UBAN GABASAWA.
Wannan kirari na Wambai, kirari ne na kasaita da isa a Gari da kuma jaruntaka wajen yaki. A cikin wannan kirari, akwai kalmomi na kasaita, kamar giye da Gari da kasa, watau ma'ana, "giye" ita ce, "abin so" , watau cin so da gari abinso da kasa, sannan taitaya Guragu, na nufin duk wanda aka cire wa kafafu ko hannaye, suka sami nakasa a wurin yaki to, wambai ke kula da su zuwa Gida tare da kula da lafiyarsu.
0 Comments