Sarautar Magajin Gari ta kafu ne a lokacin Mulkin daular Fulani amma a lokacin Mulkin Habe ana kiran ta Magajin Dangi kuma tana daya daga cikin sarautu masu mahimmanci cikin saravar 'ya'yan sarki. Wannan sarauta ta sami canji a lokacin Fulani inda suka daukaka ta suka mayar da ita sarautar 'ya'yan Sarki a kasar zazzau. Kuma aka kira ta Magajin Gari. Wanda ya fara wannan sarauta ta Magajin gari Shi ne magajin Gari malam zakari dan Malam Musa Sarkin zazzau a zamanin sarkin zazzau Malam Musa, na gidan Mallawa.
.
KIRARIN MAGAJIN GARI
" JIRGI MAI ATAGWANNI,
MAGAJI ABOKIN SARKI,
MAGAJI ABOKIN DODO,
DANO BABBA MAGAJI,
BA A MAGAJI DA YARO,
DAN UBAN GABASAWA."
Wannan shi ne kirarin Magajin Gari kuma ana fadin irin matsayinsa da daukakarsa cikin kirarinsa kamar haka, Magaji abokin Sarki, Magaji abokin Dodo. Ma'ana, ya kusanta da sarki. Sai jirgin mai atagwanne. ma'ana, mai rishi da takama kuma tun kafin ya zo akan ji amonsa (sautu).
0 Comments